YAYIN DA SHAIKH ZAKZAKY YA CIKA KWANAKI 500 A TSARE BA BISA KA’IDA BA…
A yayin da a yau Laraba 26/04/17 Jagoranmu Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky ke cika kwanaki 500 a tsare ba bisa ka’ida ba, mun fito da damanmu don mu nuna rashin jin dadinmu da ci gaba da tsare shi ba tare da wani kwakkwaran dalili ba, kuma bisa sabawar hukuncin wata kotun da ta cancanta kan lamarin.
A yayin da Shaikh Zakzaky ke cika kwanaki 500 a tsare ba tare da wata hujja ba, mun fito da yawanmu cikin lumana don nuna rashin yardarmu da yadda gwamnatin Shugaba Buhari take kallon kisan kiyashin Zariya da sojoji suka aiwatar bisa umurnin ta. Wannan shi ya janyo tsare Shaikh Zakzaky, abin da bai kamata ba tun farko tare da kisan gilla ba bisa shari’a da aka yi wa mutanen da ba su ji, ba su gani ba sama da dubu daya kuma ‘yan kasa cikin kasa da awanni 48!
A yayin da Shaikh Zakzaky ke cika kwanaki 500 a tsarewar da ba ta dace ba, mun fito ne don mu nuna sadaukarwarmu ga neman ’yancin Shehin Malamin da kuma adalci ga dukkan wadanda ake nuna masu danniya a sanadiyyar kisan kiyashin. Ba kuma za a taba tilasta mu, mu yi gum da bakunanmu ba, duk kuwa da irin matakan uzzurawa da wannan gwamnatin ka iya dauka.
A yayin da Shaikh Zakzaky ke cika kwanaki 500 a wannan tsarewar da ba ta da hujja, mun fito ne don mu nuna wa duniya cewa abubuwan da suka faru a ranekun 12-14 ga Disamban 2015, wani gagarumin gazawa ce ta wannan gwamnatin da sha rantsuwa da littafai masu tsarki cewa, za ta kare dukkan hakkokin kowane dan kasa ba tare da la’akari da kabila ko addinin da ya karkata gare shi ba.
A yayin da Shaikh Zakzaky ke cika kwanaki 500 a wannan matsananciyar tsarewar, a sarari yake ga kowa cewa, gwamnatin Tarayya ko wata daga cikin Cibiyoyinta na tsaro sun kasa fitar da wata tuhuma sahihiya a kan wannan Shugaba namu abin girmamawa. Wannan wata kwakkwarar hujja ce a fili ta kasancewarsa wanda bai aikata wani laifi ba tun asali. Ba inda aka rubuta a kundayen dokokin kasar nan cewa, za a iya tsare dan kasa har sai illa masha Allahu, ba tare da an gabatar da shi gaban kotun da ta cancanta ba.
A yayin da Shaikh Zakzaky ke cika kwanaki 500 a haramtacciyar tsarewa, yanzu fiye da kwanaki dari ke nan da wata babbar kotun Abuja ta ba da umurnin a sake shi daga hannun hukumomin da ke garkuwa da shi bisa ko ma wane irin hujja, DSS ce ko wata. Don haka abin takaici ne a ce wai gwamnatin da ke ikirarin ta dimokradiyya ce take raina umurnin kotu ba ta ko jin kunya. Raunanniyar hujjar da suke bayarwa cewa, wai sun daukaka kara kan hukuncin babbar kotun Tarayyar, ai bai nuna cewa akwai wata oda da aka bayar da ta hana aiwatar da wancan hukuncin ba.
A yayin da Shaikh Zakzaky ke cika kwanaki 500 a wannan tsarewa mara dalili, rundunar sojan kasar nan da ta aiwatar da wannan mummunan kisan kiyashin, ba abin da aka yi mata na ladabtarwa, kuma sai ta ma zabi kar ta binciki abin da ta yi a tsakanin kwanakin 12-14 ga Disamba, 2015 a yayin da ta kaddamar da wani Kwamiti da zai binciki gaskiyar zargin take hakkin dan Adam da ake mata a sauran sassan kasar nan. Wai shin menene Shugabannin rundunar sojan ke tsoro da ba za su iya bincikar mummunan kisan gillar mutane sama da dubu da suka yi a Zariya ba?
A yayin da Shaikh Zakzaky ya cika kwanaki 500 a tsarewar da ke da hadari, an hana masa hakkinsa na samun kula da lafiyar da ta dace da shi a matsayinsa ma na dattijo da ke cika shekaru 66 nan da wasu ‘yan kwanaki a hannun Buhari. Tun bayan munanan raunukan harbin bindiga da ya samu a yayin da aka tafi da shi a ranar 14 ga Disamba, 2015, ba a bar shi ya ga Likitan da ya zaba wa kansa ba, duk kuwa da cewa rashin lafiyarsa tabarbarewa take yi a kullum.
A yayin da Shaikh Zakzaky ke cika kwanaki 500 a tsarewar da ke cike da cece-kuce, miliyoyin mabiyansa da masu tausaya masa sun dage da bin tafarkin hankali da ilimi wajen cimma bukatarsu na sakin sa da gaggawa. Duk da tsangwama da takurar da wasu Gwamnoni ke mana, mun dage kan turba guda ta lumana don cimma muradunmu. Wannan kuma wata ‘yar manuniya ce ta irin koyarwar Shaikh Zakzaky wacce ba ta tashin hankali ba ce, sabanin yadda makiyansa a kullum suke kokarin shafa masa bakin fenti don dai su nuna suna da hujjar kisan kiyashin da suka aiwatar a kan ‘yan uwa musulmi na Harkar Musulunci.
A karshe a yayin da Shaikh Zakzaky ke cika kwanaki 500 a tsarewar da ka iya yin kisa, muna kira ga ‘yan Nijeriya na gari da kuma al’ummar kasa da kasa da su tilasta wa wannan gwamnatin ta Buhari ta saki Jagoranmu da matarsa da ita ma aka ji wa munanan raunuka da sauran wadanda suke tsare ba tare da wani sharadi da jinkiri ba. Ci gaba da tsare shi ba zai jawo wani alheri ba ga dukkanin mu a kasar nan da wajenta. Kuma ci gaba da tsare shin wani mummunan bata suna ne ga duk wata takamar dimokradiyya da kasar nan za ta iya yi a tsakanin kasashen duniya.
Aminci ya tabbata ga wadanda suka bi tafarkin shiriya a yayin da ake gallaza musu, suna masu hakuri.
Shaikh Abdulhamid Bello
26/04/17